Daga wannan mako za mu fara gudanar da bincike na musamman a duk mako kan abin da ya shafi wayar salula gaba dayanta. Wannan kashi na daya kenan, wanda ke kunshe da gabatarwa.
A baya babu wayar salular dake dauke da manhajar BBM sai wayar salula nau'in BlackBerry. Amma a halin yanzu bayanai na tabbatar da samuwar wannan nau'in manhaja ga masu amfani da wayoyin salula na Android. A sha karatu lafiya.
Mu'amala da wayar salula a halin tukin mota ko babur abu ne mai hadari matuka. A wannan mako za mu dubi abin da masana suka ce kan haka. A sha karatu lafiya.
Idan masu karatu basu mance ba, mun yi ta gabatar da bayanai da kasidu kan abin da ya shafi mu’amala da fasahar Intanet a wayar salula a lokuta dabam-daban. To amma har yanzu akwai sauran rina a kaba. Domin kusan a duk mako sai na samu…