A yau za mu dubi siffofin manyan babbar manhajar kwamfuta biyu na kamfanin Microsoft, da Windows XP da Windows Vista. Wannan zai taimaka wa mai karatu kara sanayya kan wadannan manhajoji masu mahimmanci.
Douglas Engelbart shi ne wanda ya kirkiri na'urar beran kwamfuta, kuma Allah ya masa rasuwa cikin 'yan kwanakin nan. A yau za mu duba tarihinsa ne da yadda aka yi ya kirkiri wannan na'ura mai tasiri.
A cikin kasidar da ta gabata makon jiya ne mai karatu ya samu bayanai kan tsarin sadarwa a tsakanin kwamfutoci, abin daa Turance ake kira Computer Networking. Bayan ‘yar gajeriyar gabatarwa, mun kawo bayani kan ma’ana da kuma nau’ukan…
Fasahar Intanet ta samo asali ne sanadiyyar musayar bayanai da kwamfutoci ke yi a tsakaninsu. Yau za mu dubi yadda kwamfutoci ke aiwatar da irin wannan sadarwa, wanda ya sauya duniya ta bangaren sadarwa.
A yau kuma ga mu dauke da bayanai, a takaice, kan kwamfuta da manhajojinta. Duk da yake wannan shi ne abin da ya kamata a ce mun fara dashi, amma dokin sanin Intanet da karikitanta ne suka shagaltar da mu. Don haka tunda mun kawo wani…
Nazari na musamman kan beran kwamfuta, wato: "Mouse" kenan. Yana cikin na'urorin da galibin mutane basu san tarihi da asalinsu ba. A sha karatu lafiya.